Korona Baros: Tsumagiyar Kan Hanya!

160
Dr. Nuruddeen Muhammad

Daga Dr. Nuruddeen Muhammad

MBBS, MWACP, FMCPsych 

Bayan na kammala duba marasa lafiya a wani yammaci, ban san lokacin da na tsinci kai na cikin tunanin irin sa’ar da na yi kasancewata cikin ƙoshin lafiya ba. A wani gefe kuwa na shiga yanayin tausayawa ga waɗanda Allah  SWT ya ɗorawa larurar rashin lafiya. Babu abun tausayi a duniya kamar maras lafiyar da bai da d’an abun hannunsa da zai nemi magani, karma a ce rashin lafiyar ta kasance ta ko a mutuce ko a yi rai. Amma mu likitoci kan ci karo da ire-iren waɗannan matsaloli a kullum, musamman ma a asibitocin gwamnati. A takaice dai, babu fa wata sana’a da za ta sa mutum ya ga tsananin talauci da kuma sheda raɗaɗinsa kamar zama Likita a Najeriya. A asibitocinmune za ka ga bil’adama ya juya bayansa yayi tafiyarsa gida da tabbacin cewa mutuwa zai yi saboda kawai bai da Naira dubu ashirin (20,000) ko dalilinta! Haka dai Malam talaka a wannan ƙasa ke mutuwarsa ke kukansa shi kaɗai. Amma fa a inda gizo ya ke saƙar shine, idan dai ba wata kiyayewar Allah SWT ta musamman ba, toh fa su kan su shafaffu da man na daf da ɗanɗana kuɗarsu! 

Cutur numfashi ta korona baros ta sako ɗan Adam a gaba. Annobar ta zama gagara badau, gobara daga kogi maganinki sai LiIlahi, duba da yadda ta fara lallasa ƙasashen da suka fi kowaɗanne ƙarfi a duniya. Cutar, ta yi ɗiban karan mahaukaciya da  ƙasashen da su ka yi fice a ƙarfin tattalin arziki, da ƙarfin makaman ƙare dangi, da ƙarfin tsarin kiwon lafiya, da kuma lafiyayyun al’umma. Korona baros dai ta zama tsumagiyar kan hanya, ki shafɗi babba ki shafɗi yaro, wadda ba ta ware bambamcin launin fata, ko ƙarfin arziki, ko kuma aƙida.

Ƙasashen yammacin turai da arewacin  Amurka, da kuma ma su arziki na nahiyar Asiya sun kere sa’a wajen kula da mutanensu da kuma son more rayuwa. Sun ɗaukaki rayuwar duniya ta yadda babu abinda suke tsoro kamar barinta. Hakan ya sa suka tsunduma cikin duniyar kimiyya  har ta kai da cewa ku san ba abun da ba su samo maganinsa ba sai dai mutuwar ita kan ta. Sun sa tsufa a gaba sai da suka rage masa gudu. Sun yi kutse cikin taswirar halittar ɗan adam (wato DNA) domin ƙera wasu daga cikin sassan jiki. Sun kuma yi tanade-tanade irin na gayawa jini na wuce domin yanayin rashin lafiya na gaggawa. Kyakkyawan misali shine; a yau a birnin New  York na Amurka an kai matakin da duk wani kira na gaggawa daga ɗan ƙasa da bai samu ɗauki cikin kimanin mintuna tara da rabi ba to tilas hukomomi sai sun bi ba’asi sun kuma ɗauki mataki na ba sani ba sabo.

Amma mu anan Najeriya za a iya cewa rashin sani (wadda ake cewa ya fi dare duhu) a tsakankanin shafaffu da man mu ya sa su tunanin cewa za su iya yin baba na ɗaka gemu na waje. Bi ma’ana, su a na su ɗan ƙaramin tunanin, za su iya son ran su yadda su ke so anan gida Najeriya, amma kuma su tsallaka Turai domin su mori waɗancan tanade tanade na lafiya ma su inganci da su turawa su ka tsarawa ta su al’ummar. Ma su hannu da shuni dai sun mai da zuwa waje domin duba lafiyarsu ya zama jiki. A matsayinka na jami’in kiwon lafiya a ƙasarnan kuwa, dole watarana sai ka haɗu da wanda zai yaɓa ma ka irin wannan batu a fuskarka. Akwai yanayin raini da wannan mutane ke da shi; mai kamar cewa ni fa waɗannan asibitocin na ku ba irin nawa ba ne. Amma fa batun gaskiya anan shine: shin idan wani abu na gaggawa ya taso makwabta za’a naimo ko kuwa abokan hulɗa da ke can nesa? Da yawa harda waɗanda za su iya ɗaukar ɗawainiyar naiman lafiya a ko ina a faɗin duniya na mutuwa kullum a ƙasarnan ta silar bugawar zuciya da sauran makamantan cututtuka. Hakan na faruwane saboda ita dai bugawar zuciya ba ta jiran lokacin da ya wuce mintina talatin zuwa awa guda, ga shi kuma mu kwata kwata ba mu da wani tsari da k’warewa, da kuma isassun kayan aikin bada taimakon farko da kuma agajin gaggawa (emergency).

Babu wani abu da zai ƙara fallasa ainahin mummunan yanayin da harkar lafiyarmu ke ciki kamar wannan annoba ta Korona Baros. Ita dai wannan cuta idan tayi tsanani ta kan maƙure numfashin mutum ne, ta hanashi shan iska saboda lalata huhu da ta ke yi. A irin wannan yanayi kuwa kusan duk marasa lafiyar na buƙatar taimakon sinadarin iskar numfashi (wato oxygen). Wa su kuwa daga cikinsu har sai an kai ga ɗorasu akan injin numfashi na bentileto (ventilator). 

Ita dai bentileto wata na’urar asibitice ta musamman mai taimakawa da numfashi wadda ke buƙatar likitoci na musamman (Anesthetics) domin sarrafa ta. Yau ƙasar Italiya ta shiga ƙarancin duka biyun, duk da kuwa cewa ƙasar na ɗaya daga cikin ƙasashe goma da su ka fi kowaɗanne ingancin tsarin kula da lafiyar al’ummarsu a duniya. Yanzu haka a arewacin ƙasar Italiyan, ƙwararrun likitocin da su kan su sun gajiya, ke yanke hukuncin wa zai rayu wa  kuma zai mutu saboda ƙarancin na’urar bentileto.

Akwai dai darussa ma su dama da amafani ga Gwamnatoci da mu kammu ƴan Najeriya da ya kamata mu kiyaye daga wancan yanayi. Na farko dai dolene muɗauki dukkanin matakan kariya domin kare kawunanmu daga kamuwa da wannan cuta. Saboda da haka, abun a yabawa hukumomine, yadda mutanenmu da ke dawowa daga ƙasashen waje ke tabbatar da ingancin tsare-tsaren da aka tanadar a duk filayen tashi da saukar jiragen sama na Ƙasa da Ƙasa da mu ke da su a faɗin ƙasarnan. Amma fa akwai sauran aiki a gabanmu

Bijirewa gwaje-gwajen da aka tanadar a filayen jiragen da wasu mambobin majalisar tarayya su ke yi ba komai bane face nuna zallar rashin wayewa da ƙarancin sanin ya kamata a fili. Hakan misaline na irin tsantsar gadara da ƙafafa na wasu daga cikin shuwagabanninmu da ke kawo bala’in da kowama sai ta shafe shi. Shugaban ƙasa Muhammad Buhari yayi dai-dai da ya aikewa duka majalisun biyu da zungureriyar takarda dake gargaɗinsu akan waɗannan ɗabi’u.  

Mu kuma ƴan Ƙasa a namu ɓangaren, dolene fa muzage dantse mu kiyaye dukkanin ƙa’idojin da masana da hukomomi su ke faɗa. Musamman ma na rage cinkoso, da yawaita wanke hannu, da kuma zama a cikin gida idan da damar yin hakan. Sannan kuma sai mu koma kan buzu domin yin addu’o’i da kuma tuba ga Ubangijinmu domin ya karemu daga wannan cuta, musamman ma irin nau’inta mai tsanani da k’asashen Amurka da Italiya ke fama da shi.

Domin kuwa a duk faɗin Najeriya fa ba mu da wannan na’urar numfashi ta bentileto (ventilator) da ta wuce guda Ɗari Biyu kacal. Sannan su kan su ɗari biyun na tattarene a manyan manyan asibitocin da ke manyan birane irin su Lagos, Abuja, Ibadan, Kano, Zaria da Fatakwal. Idan ka ɗakko wannan matsalar sannan ka ƙarata akan matsalolin asibitocinmu na yau da kullum irin na rashin wadatattu da kuma ingantattun kayan aiki da gadajen kwantar da marasa lafiya, da kuma rashin ƙwararrun ma’aikata, za ka gane cewa idan fa wannan cuta ta sakomu a gaba (Allah  ya kiyaye) kamar yadda ta saka waɗancan ma su jan kunnen, toh fa sai ɗan buzun mu! Bambamcin dai kawai shine, a wannan karon, yadda aka dama haka kowa zai sha. Domin kuwa waɗanda a da ke guduwa Turai domin neman lafiya yanzu babu gurin zuwa. Ai dama duk girman duniyarnan dai kowa ya san gidan ubansa;  duk da kuwa ƙoƙarin cureta wuri guda da a ke ta faman yi. Zuwan Korona baros kuma ya ƙara tabbatar mana da cewa giji dai lahira ce, kuma na ka dai dole sai na ka! 

Akwai ƙwararan darussa kuma marassa daɗi da za a samu bayan wannan iftil’ain ya wuce. Ala dole sai wannan gijin na mu mai suna Najeriya ya zauna ya nutsu ya kuma san inda kansa ke masa ciwo. Zuwan Covid 19 ya sa lafiya ta ƙara tabbatarwa da kowa a duniya cewa ita ce dai uwar jiki, wadda Mallam bahaushe ke cewa ‘sai da ke aka cin duniya, har ana ta marmari, har ana rawar jiki’. A saboda haka, ina da kusan tabbacin cewa duniya za ta zabura bayan wannan annobar. Za kuma ta shiga yin sabon shirin ko ta kwana – kamar yadda ta yi bayan barazanar nukiliya. Amma a wannan karon, za ta garzayane neman sabbin ilmin kiwon lafiya, da neman sani na musamman, da ƙirƙire – ƙirƙire da kuma uwa uba angiza magudan kuɗaɗe a gine ginen asibitoci da kayan aiki da horar da ƙwararru. 

Mu ma dai a Najeriya dole mu shiga taitayinmu, mu kuma tsunduma a cikin wannan gudun yada kwarin wanin da za a yi domin tabbatar da cewa ba a ci gaba da barinmu a baya ba. Yanzu dai ya rage namu mu tattara hankalinmu a wuri guda, mu kuma farka, sannan musan ina muka dosa. Lokaci yayi da za muyi watsi da son zuciyoyinmu, mu haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen yaƙar ɗai-ɗaikun banbance-banbance irin na siyasa, da ɓangaranci, da ƙabilanci dake tsakaninmu. A taƙaice dai, ba za mu taɓa iya tunkarar irin wannan ƙalubalen da ke gabanmu ba har sai mun zamto tsintsiya maɗaurin ki  guda. A cikin irin wannan yanayi, tunanin cewa idan jifa ya wuce kaina toh ya fad’a kan uban kowa fa babban kuskurene. Tunda dai jifa irinna Korona ya nuna cewa zai iya yin kwana ya dawo ya fasa kan uban kowa ma!

Amma da yardar Allah SWT za mu ga bayan Korona Baros. Sai dai ya zama wajibi mu ƙudiri niyyar yin juyin juya hali a tsarin tunaninmu da kuma a aikace domin inganta harkar kiwon lafiyarmu. Domin ita fa harkar lafiya (ba ma ta Korona ba kawai) tamkar wata tsumagiyar kan hanyace, ta shafɗi Mallam Talaka ta kuma juya ta shafɗi Attajiri.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

18 − 15 =