GWAMNATIN JIHAR JIGAWA TA SASANTA RIKICI TSAKANIN MANOMA DA MAKIYAYA A KARAMAR HUKUMAR GURI

8

Gwamnan jihar Jigawa Mallam Umar Namadi FCA, ya bayyana yadda ya sasanta tsakanin manoma da makiyaya da ke rikici a karamar hukumar Guri dake jihar Jigawa.

 Gwamnan ya ce, an sanar da shi yadda wani shugaban Fulani ya zama ƙadangaren bakin tulun dake ke da hannu dumu-dumu wajen rura wutar rikici tsakanin ɓangarorin biyu, wadda har ya yi barazanar ɗaukan tsattsauran mataki akansa.

Gwamna Namadi ya ce, ɗaukan tsauraran matakai akan lamarin abu ne da ya zama wajibi domin ceto rayukan dubban mazauna yankin wadanda rikicin yankin yake rutsa wa da su.

 Gwamnan ya yi wannan jawabi ne a lokacin da ya halarci wani gagarumin biki da aka gudanar a ranar Lahadi a rigar Boɗala a karamar hukumar Guri domin murnar wanzuwar zaman lafiya a yankin.

 Gwamnan wanda yake jawabi cike da annuri, ya ce an samu sulhu a tsakanin ɓangarorin biyu bayan ƙulla yarjajjeniya da Lamiɗo Gide wanda da farko ya ke da kuskuren fahimtar zaman lafiya tsakanin al’umma.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

19 − fourteen =