DALIBAN MAKARANTAR KURIGA DA ‘YAN BINDIGA SUKA SACE SUN SHAKI ISKAR ‘YANCI

43

‘Yan bindiga sun Sako dalibai 287 da suka sace a Kuriga dake karamar hukumar Chikun ta Jihar Kaduna,bayan sun shafe kwanaki 16 a hannun su.

Gwamnan Jihar Kaduna Uba sani shine ya sanar da sakin yaran a shafin sa na Facebook.

sai dai gwamnan bai yi wani karin bayani dangane da sakin yaran ba, amma ya yabawa shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, da mai baiwa shugaban kasar shawara kan tsaro Nuhu Ribadu, da Kuma dakarun sojin Najeriya.

A ranar 7 ga watan Maris ne ‘yan bindigar suka yi awon gaba da daliban a makarantar Firamare da karamar Sakandire dake Kuriga a Jihar Kaduna.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

six + two =