Wasan Najeriya da Ghana: an umarci ma’aikata su tashi aiki karfe 1

67

Gwamnatin tarayya ta bada umarnin tashi daga aiki a gobe Talata ƙarfe ɗaya, don kallon wasan Najeriya da Ghana.

Cikin wata sanarwa da ofishin shugaban ma’aikata na tarayya ta fitar, ta bayyana cewa tashi daga aikin zai zamo ne don tattaro magoya baya ga ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Najeriya, super Eagles.

Wasan da za a buga, wasa ne na share fage zuwa wasan cin kofin duniya da zai gudana a ƙasar Qatar.

Takar dar sanarwar

Sanarwar kuma ta nemi duk manyan sakatarorin hukumomin gwamnati da su yaɗa sanarwar tashi daga aikin ga ma’aikatunsu.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

twelve − 10 =