HUKUMAR EFCC TA KAMA MOTOCIN DAKON KAYA 21 MAKARE DA KAYAN ABINCI A HANYAR N’DJAMENA NA KASAR CHADI

2

Hukumar dake yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta Najeriya EFCC ta sanar da kama motocin dakon kaya 21 maƙare da kayan abinci da wasu kayayyaki da ke kan hanyar N’djamena a jamhuriyar Chadi da jamhuriyar tsakiyar Afirka da Kamaru.

Hukumar tace an kama manyan motocin ne yayin wani samame da aka ƙaddamar kan titunan Kalabiri/Gamboru Ngala da Bama a jihar Borno.

Binciken da aka gudanar ya nuna wasu kayan abinci da aka yi dabarar ɓoye su cikin motocin da za su iya wucewa ba tare da an gano ba.

Dama dai shugaban hukumar hana fasa ta kasa ya sanar da kokarin hukumar a wannan aikin, in da suka cafke irin wannan motocin 121 a ‘yan makonnin nan.

Ana sa ran kamen motocin zai kawo ƙarshen matsalar abincin da ake fama da shi sakamakon yadda wasu ke fasaƙwabrinsa.

Ana gudanar da bincike kan mutanen da ake zargi kuma za a gurfanar da su a gaban kotu da zarar an kammala bincike.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

eleven − 8 =