GWAMNATIN NAJERIYA TA TILASTA AMFANI DA DOKAR HARAMTA FITAR DA ABINCI

4

Gwamnatin Najeriya ta bada umarnin tilasta amfani da dokar haramta fitar da kayan abinci daga Najeriya domin tabbatar da samar da wadataccen abinci a fadin kasar nan.

Wannan na zuwa ne bayanda hukumar samar da abinci da aikin gona ta majalisar dinkin duniya ta yi hasashen cewa ‘Yan Najeriya Milyan 31.5 a fadin Jihohin kasar nan 26 zasu iya fuskantar matsanancin karancin abinci daga watan Yuni zuwa Agusta na wannan shekara.

Kwanturola Janar na hukumar hana fasakwauri ta kasa Kwastam Bashir Adeniyi Adewale, shine ya bayyana haka yayin ganawa da manyan ‘yan kasuwa a kasuwar kayan abinci ta Dawanau dake Kano,yace hukumar na kokarin magance duk wani yunkuri da zai kawo cikas ga tattalin arziki da kuma magance yunwa da karancin abinci a fadin kasar nan.

Mista Adewale, ya fadawa manyan ‘Yan kasuwar na Dawanau cewa sun karbi umarni haramta fitar da kayan abinci daga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu,musamman a wannan lokaci da ‘Yan kasa ke fama da matsalar karancin abinci.

Yace hukumar hana fasa kwauri ta kasa kwastam zata aike da jami’an ta domin hana fitar da kayan abinci daga Najeriya kamar, shinkafa, wake,dawa,masara,hatsi da sauran kayan abinci.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

nineteen + fifteen =