IMF YA BUKACI GWAMNATIN NAJERYA TA BADA FIFIKO WAJEN SAMAR DA ABINCI

3

Asusun bada lamuni na duniya IMF yace ya zama wajibi gwamnatin tarayya ta bada fifiko wajen samar da abinci a kasar nan.

IMF ya fitar da wannan rahoto ne karkashin jagorancin babban jami’in bankin a Najeriya Schimme Fennig, bayan sun kai ziyarar aiki Jihohin Legas da babban birnin tarayya Abuja domin tattaunawa da kuma tuntubar gwamnatin tarayya.

Asusun bada lamunin na duniya yace matakin da kwamitin manufofin kudi na babban bankin kasa ya dauka domin karfafa tsarin kudade zai taimaka matuka wajen shawo kan tashin farashin kayayyaki da karyewar darajar kudin Naira.

Yanzu haka dai ana fama da tashin gwauron zabbin kayayyaki da canjin kudaden waje da tsadar rayuwa, da janye tallafin man fetir ya haifar lamarin da janyo zanga-zanga a wasu sassa na kasar nan.

Darajarar kudin kasar nan Naira yayi karyewar da bai ta ba yi tun bayan da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya shiga Ofis watanni tara da suka gabata.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

3 × 2 =