MINISTAN KUDI NA NAJERIYA YA DORA ALHAKIN HAUHAWAR FARASHI KAN GWAMNATIN BUHARI

5

Ministan kudade da tsare-tsaren tattalin arziki Wale Edun,ya dora alhakin hauhawar farashin da ake fuskanta a kasar nan kan buga Tireliyoyin Naira da gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari tayi.

Ministan ya bayyana haka ne yayin ganawa da kwamitin kudi na majalisar dattawa.

Mista Wale Edun yace ma’aikatar ta shirya bin diddigin yadda aka buga Kudi Naira Tiriliyan 22.7 a lokacin da godwin Emefiele yake gwamnan babban bankin kasa CBN.

Yace kudin da aka buga a karkashin shirin Ways and Means na gwamnatin tarayya daga shekarar 2015 zuwa 2023 ya haifar da hauhawar farashin a Najeriya.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

2 × one =