Gwamnatin Katsina ta kashe miliyan 175.5 wajen gyara filayen wasanni 2

68

Gwamnatin Jihar Katsina tace ta kashe jumillar kudi naira miliyan 175 da dubu 500 wajen gyara filayen wasanni biyu a jihar.

Kwamishinan wasanni da walwala na jihar, Sani Danlami, ya sanar da haka ranar Laraba a Katsina lokacin da yake lissafa nasarorin da ma’aikatarsa ta samu.

Sani Danlami yace an kashe jumillar kudi naira miliyan 111 da dubu 300 wajen gyara da d’aga martabar filin wasanni na Malunfashi, yayin da aka kashe naira miliyan 64 da dubu 200 wajen karasa aikin dandalin wasanni na Katsina wanda aka yi watsi da shi.

Kwamishinan yayi bayanin cewa an gudanar hakan da nufin habaka harkokin wasanni tsakanin matasa a jihar.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

3 + two =