Kotu ta garmake Sufeto Janar na ‘Yansanda Usman Baba

29

Wata babbar kotun tarayya dake zama a Abuja a yau ta zartar da hukuncin kulle Sufeto Janar na ‘Yansanda, Usman Akali Baba, tsawon watanni uku bisa kin bin umarnin hukuncin wata kotu na mayar da wani dansanda mai suna Patrikc Okoli bakin aiki, bayan anyi masa ritayar dole.

Mai Shari’ah Bolaji Olajuwon, a wani hukunci da ya yanke akan karar da lauyan Patrick Okoli mai suna Arinze Egbo ya shigar, ya kuma gargadi Usman Baba akan bin umarnin hukuncin kotun farko.

Mai Shari’ah Bolaji Olajuwon yayi gargadin cewa idan sufeto janar din ya kasa wanke kansa daga kin bin umarnin, za a iya sake zartar masa da wani hukuncin na daurin watanni uku.

Patrick Okoli ya kai karar sufeto janar din a gaban kotu a matsayin wanda yake tuhuma.

Mai karar, wanda ya nemi kotun da ta bayar da umarnin a mayar da shi aikinsa, yace hukumar kula da ayyukan ‘yansanda ta kasa ce ta yi masa ritayar dole ba bisa ka’ida ba a shekarar 1992, lokacin da yake aiki a rundunar ‘yansandan jihar Bauchi a matsayin CSP.

A wani labarin kuma, jami’an rundunar ‘yansandan babban birnin tarayya a yau sun tarwatsa daruruwan masu zanga-zanga dake neman murabus din alkalin alkalan Najeriya na kasa, Mai Shari’a Olukayode Ariwoola, bisa zargin ya dauki bangare a babban zaben 2023.

Idan za a iya tunawa dai, Mai Shari’a Ariwoola a wajen wani biki da gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike ya shirya domin karrama shi a Fatakwal, yace yana farincikin kasancewar gwamnansa, Seyi Makinde na jihar Oyo yana tare da Nyesom Wike a kungiyar G5 ta gwamnonin PDP.

Masu zanga-zangar, a karkashin gamayyar kungiyoyin fararen hula na kasa, sun ce matsayar da alkalin alkalan ya dauka tana da hadari wajen gudanar da shari’ar gaskiya a rigingimu gabannin, lokacin da bayan babban zaben 2023.

Da yake zantawa da manema labarai yayin zanga-zangar, kakakin gamayyar, Olayinka Dada, yayi kira ga alkalin alkalan da ya sauka daga mukaminsa domin tabbatar da mulkin demokradiyya a kasarnan.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

four × four =