Gwamnatin Tarayya Ta Sake Bibiyar Dokar Hana Fita Bayan Karin Mutane 35 Sun Kamu Da Covid-19 Inda Yawan Wadanda Suka Kamu Ya Kai 174 A Kasarnan

33

Gwamnatin Tarayya ta sassauta dokar hana fitar da ta kakaba a babban birnin tarayya da jihoshin Lagos da Ogun, domin dakile yaduwar covid-19.

Gwamnatin, a wasu sabbin ka’idoji data fitar ranar Laraba, ta bayyana cewa za a bude kasuwannin dake sayar da kayan abinci daga karfe 10 na safe zuwa 2 na rana, fashin kwana dai-dai.

Kazalika, za a bude manyan shagunan sayayya da shagunan magunguna  daga karfe 10 na safe zuwa karfe 4 na yammacin kowace rana, amma dole su zamto cikin yanayin tsafta sosai.

Sabbin ka’idojin sun kuma haramta hayar mota lokacin hana fitar. Haka kuma an hana taruwar mutane sama da 20.

Gwamnatin tarayya ta sake bibiyar dokar hana fitar jiya Laraba bayan yawan mutanen da suka kamu da Covid-19 sun karu da 35 inda suka kai 174 a kasarnan.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

five × five =