Hukumar Kula da Wutar Lantarki Ta Amince Da Karin Kudin Wuta

26

Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Najeriya ta amice da karin kudin wutar da kamfanonin rarraba wutar lantarki 11 na kasarnan suka yi.

Kamfanin Dillancin Labarai na kasa ya bayar da rahoton cewa sabon karin kudin wutar na kamfanonin wanda ya shafi masu amfani da wutar rukuni-rukuni, an wallafa shi a shafin yanar gizon hukumar.

Umarnin ya samu sa hannun shugaban hukumar, Farfesa James Momoh, da sakatare, Mista Dafe Apedeye.

Hukumar tunda farko tace umarnin ya shafe wanda ya gabata, kuma karin kudin wutar ya fara aiki daga ranar 1 ga watan Janairun da muke ciki.

Hukumar tayi nuni da cewa za a kula da umarnin da sauran sauye-sauye tare da yawan wutar da ake samarwa tun daga ranar 31 ga watan Oktoban 2019.

Hukumar kula da wutar lantarkin tace masu amfani da wutar a yanzu za suke biyan karin naira 19.89 kowane unit, wato karin kashi 236.75 cikin 100.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

1 × two =