HUKUMAR NACA TACE MUTANE 6 DAGA CIKIN MUTU 1O DA SUKE DAUKE DA CUTAR AID MATA NE

2

Hukumar yaki da cuta mai karya garkuwar jiki ta kasa NACA tace mutane 6 daga cikin mutum 10 da suke dauke da cutar mata ne.

Hukumar ta bayyana hakan ne a bikin ranar mata ta duniya,inda ta yi bayanin cewa rayuwar mata tafi fuskantar barazanar kiwon lafiya har sau uku idan aka kwatanta da takwarorin su maza a shekaru.

Babban daraktan hukumar Gambo Aliyu, yace hukumar na kokari wajen tabbatar da samar da dai-daito a tsakanin mata da maza tare da magance kalubalan da suke fuskanta musamman mata masu dauke da cuta mai karya garkuwar jiki.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

15 + 9 =