Gwamnatin jihar Jigawa ta haramta hawa babur

739
Gwamnan Jihar Jigawa Badaru Abubakar

Gwamnatin jihar Jigawa ta sanar da haramta amfani da babur daga karfe 9 na dare zuwa 6 na asuba a fadin jihar baki daya, da nufin dakile matsalar rashin tsaro dake karuwa a wasu yankuna na jihar.

Sanarwar hakan na na kunshe ta cikin sanarwar da shugaban karamar hukumar Dutse kuma shugaban kungiyar ALGON na jihar, Alhaji Bala Usman Chamo ya fitar.

Ya bayyana cewa an dauki matakin ne a yayin zaman da aka gudanar kan sha’anin tsaro wanda gwamna Muhammadu Badaru Abubakar ya jagoranta.

Bala Usman ya bayyana cewa hana amfani da babura wani bangare ne na kokarin gwamnatin jihar na dakile masu amfani da babura domin aikata laifukan ta’addanci, musamman a yankunan karkara.

Haka kuma ya kara da cewa an sanar da shuwagabannin ‘yan achaba wannan matakin domin su sanar da mambobin su. Haka kuma ya kara da cewa an sanar da hukumomin tsaro wannan matakin domin su tabbar ana bin dokar kamar yadda hukumomi suka tanada.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

11 + 14 =