TASIRIN MAHAIFA GA YA’YA A YAYIN KOYAR DABI’UN SU

38
SKY Daily Hausa

Daga Garba Sidi

Kamar yadda Allah ya halicce mu ta hanyar mahaifa guda biyu daban-daban, Kuma ya sanya hakkokin kula da mu a hannun su. Dabi’un su nada matukar tasiri ga ya’ya kama daga haihuwar su zuwa girman su, kamar yadda Malami akan halayyar Dan Adam ABUBAKAR SADIK HARUNA yayi bayani a littafinsa mai suna “A SIMPLE GUIDE IN PSYCHOLOGY“.

wannan ya sanya halayyar mu tasha bam-bam data juna. Baya yiwuwa ace dukkan abinda kake so haka sauran al’umma suke so, dalilin da yasa ake samun wani mai hakuri, wani marar hakuri, wani mai gaskiya,wani marar gaskiya. To dukkan wadan nan halaye tasirinsu yana da alaka da Abubuwa da dama Amma Mafi tasiri aciki sune Mahaifa.


Bincike da dama ya tabbatar da yaro na gadon dabi’un mahaifansa guda biyu. Dayawa daga abinda muke so, da wadan bama so, mahaifa nada tasiri akan su gare mu.  Yawan cin halaye da dabi’u  mahaifa  ke koyar da su, duk da akan yasar da wasu yayin da aka girma ko Kuma wani yanayi ya samu. Mahaifa kan koya wannan dabi’u ne ta hanyar  bada labari ko yin bayanin mutane, Abubuwa, siyasa ,fasaha da Kuma abubuwan da suka faru mai dadi da marar dadi, sune ke nunawa yaro munin halayya da Kuma kyawawan dabi’u. Anyi ittifakin hatta addini yaro yakan taso da addinin daya tarar mahaifan sa sunayi, kamar yadda Malami akan dabi’ar dan Adam Marigayi MUHAMMAD GISHIWA Ph.D yayi bayanin a littafinsa mai suna “AN INTRODUCTION TO EDUCATIONAL PSYCHOLOGY”.


Mahaifa sune mutane na farko da yaro yake fara mu’amalanta, hakane ya sanya suke Koya masa magana, kaga kenan hatta kalmomi da yaro zaina furtawa mahaifan sa ke koya masa su kafin kowa yaji su. Kamar yadda ETETE CHUKWUMA A. yayi bayanin jakadun halayya da dabi’u a littafinsa  mai suna “MORAL PHILOSOPHY“.   Wannan ya nuna duk yayin da aka samu matsala daga dabi’un yaro to, ta faro ne daga mahaifan sa. 

Malam Sidi ya iko da wanan ra’ayin nasa ne daga garin Hadejia, jihar Jigawa

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

15 − 7 =