Mutane 26 sun mutu bayan jirgin ruwa ya kife a Sokoto

171

An tabbatar da mutuwar mutane 26 yayin da ake cigaba da neman wasu biyo bayan kifewar wani jirgin ruwa a kogin Shagari dake yankin karamar hukumar Shagari ta jihar Sokoto.

Shugaban karamar hukumar Shagari, Aliyu Dantani, wanda ya sanar da lamarin a yau ga kamfanin dillancin labarai na kasa a Sokoto, yace hatsarin ya auku a jiya da yamma.

Aliyu Dantani yace daga cikin gawarwaki 26 da aka gano, 21 mata ne, yayin da 5 yara ne, inda ya kara da cewa ana cigaba da binciken wasu gawarwakin.

Sai dai, shugaban karamar hukumar yace har yanzu ba a tantance ainihin yawan fasinjojin da ke cikin jirgin ruwan ba.

A cewarsa, yanzu haka akwai mutane dayawa a cikin ruwa dake kokarin ceto wadanda basu mutu ba tare da samo gawarwakin wadanda suka mutu.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

thirteen + fifteen =