Kwamitin Rabon Arzikin Kasa ya raba N606bn na watan Mayu

20

Kwamitin rabon arzikin kasa a jiya yace ya raba jumillar naira miliyan dubu 605 da miliyan 958 a matsayin kudaden watan Mayun da ya gabata, ga gwamnatin tarayya da jihoshi da kananan hukumomi da wasu hukumomi.

Daraktan yada labarai a ma’aikatar kudi, kasafin kudi da tsare-tsaren kasa, Charles Nwodo, cikin wata sanarwa a Abuja, yace an raba kudaden a lokacin zaman kwamitin da aka gudanar ta bidiyo.

Kwamitin, a takardar bayan taro, yayi nuni da cewa kudin naira miliyan dubu 605 da miliyan 958 da aka raba ya hada da kudaden da aka samu daga hukumar hana fasa kwauri da hukumar albarkatun man fetur da kuma hukumar tara kudaden shiga.

Kwamitin ya kuma sanar da cewa, a rabon gwamnatin tarayya ta samu naira miliyan dubu 242 da miliyan 120, jihoshi sun samu naira miliyan dubu 194 da miliyan 195, yayin da kananan hukumomi suka samu naira miliyan dubu 143 da miliyan 742.

Ya kara da cewa jihoshin da ake hakar man fetur sun samu karin miliyan dubu 26 miliyan 901.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

3 + 14 =