DAWOWAR KWANKWASO APC, BARAZANA GA GWAMNA GANDUJE

75

Daga Bashir Abdullahi El-Bash

-Yaya Alaƙar Siyasa Ta Ke Tsakanin Kwankwaso Da Ganduje A Jiya Da Yau ?

-Yadda Jita-Jita Ta Yi Ƙarfi Kan Iyuwar Dawowar Kwankwaso APC A Karo Na Biyu.

-Wacce Barazana Gwamna Ganduje Zai Fuskanta, Wacce Moriya APC Za Ta Samu Idan Ta Tabbata Kwankwaso Ya Sake Dawo APC ?

Tun bayan samun bayanin komawar gwamnan Jihar Zamfara jam’iyyar APC jita-jita da raɗe-raɗi ke zagayawa a kafofin sadarwa na zamani cewa shirye-shirye sun yi nisa na dawowar tsohon gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso a karo na biyu zuwa jam’iyyar ta APC wacce ya aura ya saka.

Sai dai har zuwa yau babu bayani a hukumance daga shi Kwankwason ko uwar jam’iyyar APC ta ƙasa da ta Jiha dangane da gaskiyar wannan batu. Duk da haka jita-jitar na ƙara ƙarfi kuma babu bayanin musantata daga ɓangarorin biyu kamar yadda babu bayanin gaskata ta. Duba da wannan, zan karkatar da hasashena zuwa ga batun iyuwar sake komawar Kwankwaso cikin jam’iyyar APC, sannan idan hakan ta tabbata wanne ƙalubale ko barazana ce za ta fuskanci mai girma gwamna, Dakta Ganduje ?.

Kamar yadda wasu su ka sani, akwai daɗaɗɗiyar alaƙar siyasa tun zamanin mulkin soja na Abacha a tsakanin Kwankwaso da Ganduje a lokacin Ganduje ya na matsayin kwamishinan ayyuka, Kwankwaso kuma ba kowa ba ne a gwamnati har zuwa 1999 da aka dawo dimokaraɗiyya Kwankwaso ya samu nasarar zama ɗan takarar gwamna a jam’iyyar PDP. Tsawon wannan lokaci alaƙar zamantakewar siyasa ta na faruwa a tsakanin Kwankwaso da Ganduje babu wata matsala a tsakaninsu har su ka jagoranci Jihar Kano tsawon shekaru 8 Kwankwaso na gwamna, Ganduje mataimakin gwamna inda daga ƙarshen zango na biyun a shekarar 2015 Ganduje ya gaji kujerar gwamnan.

Sai dai kuma dangantaka ta fara yin tsami a fili a tsakanin aminan biyu a shekarar 2016 lokacin da tsohon gwamna Sanata Kwankwaso ya je garin Ganduje ziyarar ta’aziyyar rasuwar mahaifiyar gwamna Ganduje inda aka zargi Kwankwason da maida ta’aziyyar gangamin siyasa tare da shiga garin da ƴan daba su na zage-zage da rera waƙoƙin yabo ga Kwankwaso kan shugabancin ƙasa.

A wannan lokaci hatta shugabancin jam’iyyar APC na Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Umar Doguwa sai da su ka yi barazanar ɗaukan matakin ladaftarwa ga Kwankwason saboda waccar rashin ɗa’a da ake zargin shi ne ya tunzura magoya bayansa su yi. Ko da yake, a nasu ɓangaren ƴan Kwankwasiyya sun musanta wannan zargi tare da ɗora laifin faruwar abin ga waɗanda su ka nemi takara ba su samu ba domin su haddasa fitina da kunna wutar gaba a tsakanin Kwanlwason da Gandujen.

Koma dai minene mai faruwa ta riga ta faru, domin tun daga wannan lokaci har zuwa yau wutar gaba da ƙiyayyar juna ke cigaba da ruruwa a tsakanin ɓangarorin biyu. 

A shekarar 2020 ya yin da Gwamna Ganduje ya karɓi tawagar Rabi’u Suleman Bichi waɗanda su ka bar Kwankwasiyya su ka koma Gandujiyya, a cikin jawabinsa ya shaida cewa Kwankwaso ya fara adawa da shi tun ma kafin a yi zaɓe ya zama gwamna a shekarar 2015 domin kuwa Kwanwaso ne ya ke ce cewa “Idan waɗanda mu ka tsayar ba su yi abin da mu ke so ba, to za mu ɗage ƙafar wando mu kore su”. Sannan har Ganduje ya gama zagayen kamfen Kwankwaso bai tafa fita kamfen ba, haka nan bai ba da ko sisi ba, hasalima darakta kamfen da Ganduje ya naɗa Kwankwaso cewa ya yi bai yarda ba. Ire-iren waɗannan abubuwa da Ganduje ya ce Kwanwaso ya yi masa, su ke nuni da cewa tun asalima Kwankwaso bai so Gandujen ya zama ba, ƙaddara ce kawai ta faɗa, sannan tun daga nan dangantakar ta fara tsami.

Tuni an daɗe da raba garin jam’iyya a tsakanin Kwankwaso da Ganduje, sai gashi kuma ana raɗe-raɗin Kwankwason zai sake dawowa ƙarƙashin inuwar da Gandujen ya ke. 

Idan hakan ta tabbata, akwai babbar barazana a gaban Ganduje. Na farko dai kamar yadda kowa ya sani, mafi yawan mutanen da ke tare da gwamna Ganduje a yanzu su na tare da shi ne saboda kujerar gwamna, a duk lokacin da tabbata Kwankwaso zai dawo APC duk waɗannan mutanen da ke tare da shi don kujerarsa za su fara ƙaura su na zuwa kamun ƙafa wurin Kwanwaso a fili ko a ɓoye, za a fara bijirewa umarninsa da yi masa bita da ƙulli domin sun riga sun san wa’adin mulkinsa ya riga ya ƙare, shi kuma Kwankwaso babu yadda za a yi ya dawo jam’iyyar APC ba tare da wani alƙawari mai ƙarfi daga sama ba, ƙila a ba shi ragamar jam’iyyar a Jihar sai yadda ya yi da ita, to wannan tunani shi zai sanya mutane da yawa su butulcewa Ganduje ko da za su cigaba da zama da shi to zai kasance masu yi masa zagon ƙasa ne da biyayyar ƙarya wacce dama akan ta su ke ba don Allah su ke son sa ba sai dan kujerar.

Idan kuma gwamna Ganduje ya na da burin neman takara ko ta sanata, to idan Kwankwaso ya dawo jam’iyyar burin nasa zai iya samun tawaya duba da tsamin dangantakar.

Baya da wannan, Kwankwaso ɗan siyasa ne mai farin jini da yawan mabiya a Jihar Kano da ma sassan Arewa, jam’iyyar APC za ta ribaci cin moriyar yawan mabiyansa idan ya koma cikinta, su kuma za su yi ƙoƙarin cika masa dukkan wani alƙawari ko burinsa domin su ribaci waccar dama a zaɓen 2023.

Koma dai mai ne ne, masu karin magana sun ce wai kwai da dutsi ba sa haɗuwa wuri guda kamar yadda ruwa da wuta ba sa yi. Mawuyacin abu ne Sanata Kwankwaso da Gwamna Ganduje su sake haɗuwa a inuwar siyasa ɗaya, ko sun haɗu to masu cin abinci da rigimar sai sun ƙara farraƙa su, duba da wannan idan ta tabbata Kwankwaso zai koma APC to dole gwamna Ganduje ya shiryawa wannan ƙalubale da ke gabansa, ko dai ya gudu ya bar jam’iyyar kamar yadda kwankwason zai gudo daga wata jam’iyyar idan ta tabbata, ko kuma ya yi nazarin tunkarar wannan barazana da ka iya ƙarya alƙadarin siyasarsa. Ko kuma Kwankwaso ya cigaba da zama a inda ya ke gwamna Ganduje ya cigaba da jan ragamar jam’iyyar a Jihar Kano masu biyayyar ƙarya da masoyan gaske su cigaba da binsa ya dama duk yadda ya ke so a 2023.

El-Bash ya rubuto wannan ra’ayin nasa daga jihar Kano.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

three × two =