NNPC ya ce Najeriya na asarar danyen mai na N151.78 biliyan kowane wata

8

Kamfanin Mai na Kasa NNPC ya sanar da cewa a halin yanzu Najeriya na asarar akalla gangar danyen mai dubu 200 kowace rana.

Farashin danyen mai na Brent yana Dala 66.75 kowace ganga a jiya, yayin da ake sayar da Dala daya akan Naira 379 farashin gwamnati.

Daga alkaluman sama, ya nuna cewa Najeriya na asarar kimanin Naira miliyan dubu 151 da miliyan 790 cikin kwanaki 30, idan aka yi la’akari da ganga dubu 200 da aka asara a kowace rana kamar yadda kamfanin NNPC ya sanar.

Shugaban Kamfanin na NNPC, Mele Kyari, ya sanar da yawan danyen man da ake asara kullum a Najeriya, lokacin da yake jawabi a jiya a wajen zaman ganawa da babban hafsan tsaro na kasa, Manjo Janar Lucky Irabor.

A nasa bangaren, Irabor yayi alkawarin zaburar da sojoji domin su samar da cikakken tsaro kan guraren mai da iskar gas na kasa.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

18 − 11 =