Sufeto Janar na ‘Yansanda, Mohammed Adamu, ya bayar da umarnin sakin ‘yansanda masu tsaron lafiyar uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari, kwanaki 4 bayan an rufe su bisa harbin bindiga a fadar shugaban kasa dake Abuja.
Lamarin ya haifar da kokwanton cewa ko rayuwar shugaban kasa Muhammadu Buhari na cikin hadari.
Amma fadar shugaban kasa a cikin wata sanarwa ta tabbatar da cewa Shugaba Buhari baya cikin wani hadari a kowane lokaci.
‘Yansandan sun hada da ADC na Aisha Buhari, CSP Usman Shugaba; da kwamandan rakiyarta, DSP Sheriff Kazeem da yansandan kwantar da tarzoma 4, an tsare su ranar Juma’ar da ta gabata.
An umarce su da su koma a yau domin cigaba da bincike.