Shugaba Buhari ya halarci daurin auren dansa a jihar Kano

111

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a yau ya halarci daurin auren dansa, Yusuf Muhammadu Buhari, a masarautar Bichi dake jihar Kano.

Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar na daga cikin jiga-jigan mutanen da suka halarci daurin auren na Yusuf Buhari tare Zahra Nasiru Bayero, ‘yar sarkin Bichi.

Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki, Ali Isa Pantami, ya daurawa ma’auratan aure a babban Masallacin Bichi bayan an biya naira dubu 500 a matsayin sadaki.

Dan dan’uwan Shugaba Buhari, Malam Maman Daura, shine waliyyin ango, a madadin shugaban kasa, yayin da fitaccen dan kasuwa, Alhaji Aminu Dantata, ya zama waliyyin amaryar a madadin dangin Bayero.

Manya manyan mutane sun halarci daurin auren, wanda aka shafe tsawon makonni ana zancensa.

Gwamnoni, ministoci, sanatoci da manyan ‘yan kasuwa maza da mata sun kasance a Bichi domin bikin.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

11 − one =