An kashe gomman mutane a wani sansani a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo

23

Kimanin mutane 60 da ke zaune a sansanin marasa galihu ne suka mutu a wani mummunan hari da aka kai cikin dare a arewa maso gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo.

Wasu mutane dauke da bindigogi da adduna sun kai farmaki sansanin da aka kafa domin wadanda aka tilastawa barin gidajensu a lardin Ituri saboda rikicin kabilanci.

Basaraken yankin ya ce yawancin wadanda abin ya shafa mata ne da kananan yara. Yawancinsu an yanka makogwaronsu.

An zargi mayakan kungiyar Codeco da aikata kisan.

Mayakan kungiyar sun fito ne daga al’ummar manoman Lendu, wadanda ke rikici da makiyayan Hema na lardin.

Kimanin mutane miliyan 1 da dubu 700 ne aka tilastawa barin gidajensu a Ituri tun lokacin da tashe-tashen hankula suka fara kamari shekaru da dama da suka gabata.

A wani labarin mai alaka, akalla mutane 26 ne suka mutu bayan da wata igiyar wutar lantarki da ta fado kansu a wata kasuwa a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango.

Babbar igiyar wutar lantarkin ta tsallaka ta fada kan gidaje da mutanen da ke sayayya a yau kusa da Kinshasa babban birnin kasar.

Hotunan da ba a tantance ba da aka yada a shafukan sada zumunta sun nuna yadda lamarin ya faru, tare da wasu gawarwakin da ba sa motsi a cikin kududdufai na ruwa.

Har yanzu ba a bayyana dalilin da ya sa wayar wutar lantarki ta tsinke ba.

Sai dai a wata sanarwa da kamfanin samar da wutar lantarki na Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango ya fitar, ya ce ya yi amanna cewa walkiya ta afkawa igiyar, lamarin da ya sa ta fadi kasa.

‘Yan sanda sun ce lamarin ya faru ne a gundumar Matadi-Kibala da ke wajen birnin Kinshasa kuma mutane da dama sun mutu nan take.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

15 + 10 =