Ƙalubalen Matasan Hausawa a Ƙarni na Ashirin da Ɗaya

112

Daga Ameer Muhammad Harbo 

Da yawan mutane sun sani cewa ana murnar wannan ‘Ranar Hausa’ a wannan rana ta 26 ga watan Agusta a kowacce shekara. Hakan yana bada dama domin tattauna maudu’i kala-kala ta bangarori daban-daban da ya shafi harshen Hausa da kuma Hausawa.

Duk da cewa harshen Ingilishi (Turanci) na karanta a Jami’a hakan bazai hanani yin tsokaci ga asalin harshe na ba wanda nake tinƙaho da taƙama da alfahari da kuma tutiya dashi, musamman ta bangaren gudunmawar matasa a wannan zamanin da muke ciki.

Hausawa suna cewa yayin bikin farar kaza balbela ance ba gayya ba ce, sabo da haka dole na ambato Farfesa Abdalla Uba Adamu wanda ya haɓaka nau’ikan harshen na Hausa (Ɓɓ, Ɗɗ, Ƙƙ), waɗanda ada basu kasance a Intanet ba. Na jinjina maka!

Sanin kowa ne ‘matasa’ sune jigo a wajen cigaban kowanne yanki ba ma iya yankin Hausawa ba, a’a, a ma kowanne nahiya. A haƙiƙanin gaskiya akwai ƙalubale da dama da suke barazanar yi wa harshen na Hausa tashin tantabarun Hudu a wannan zamani. Daɗi da ƙari harma da al’ummar Hausa na fuskantar waƴannan ƙalubale na ƙarni na ashirin da ɗaya.

Idan nace zan gutsuro daga cikin tarihi, zamu gane ƙoƙarin dasu Sardaunan Sakkwato suka yi wajen haɓaka Yaren da kuma al’adar Hausawa, domin an fara buga jaridar Hausa ta farko, wato “Gaskiya Ta Fi Kwabo” a cikin 1938. Wannan tabbas ya bada gudunmawa ga harshen Hausa, domin ya shiga gaban sauran harsunan Najeriya har zuwa wannan lokacin. Wannan ƙalubale ne da ya kamata a samu masu kishin Hausa waƴanda zasu ɗora da yi masa hidima kamar na wancan lokacin. Saboda haka wannan ƙalubale ne da yake kan kowa harma da shuwagabanni da malamai da matasa.

Abunda ya zamar wa Hausawa tukin tuwon tulu shine “westernization” a turance, sabo da yawan matasan mu a wannan ƙarni suna ɗaukar yin al’adar Bature shine wayewa ko kuma cigaba a duniyar su ta gidadanci (ma’ana civilisation). Hakan yasa sun yasar da al’adar Hausawa mai inganci wadda muka gada.

Haka zalika, yana ɗaya daga cikin ƙalubalen da harshen Hausa da Hausawa suke ciki sai kaga matashin Bahaushe ya gama sakandare koma jami’a amma bai iya Hausar bama a baki sosai ballantana rubuta ta da inganci. 

Ya isa matasan mu misali idan muka duba rayuwar Alhaji Dr. Abubakar Imam wanda yana da shekara 22 ya rubuta shahararren littafin nan mai suna “Ruwan Bagaja”. Bisa wannan yasa ina da wasu ƙudirai masu kyau a zuciya ta wanda nakeso Allah ya taimake ni a kansa. 

Bugu da ƙari, yawancin tallace-tallacen da Hausawa suke a ko ina idan muka duba zamu ga a yaran Ingilishi akeyin su, in kuma da Hausa akayi to waƴanda ba Hausawa bane suka yi.
Ko da yake Turanci ya riga ya yi ƙaƙa-gida a kasar Hausa musamman birane – waƴanda babu ruwansu da kishin yaren na Hausa. Wannan yana faruwa tun daga rashin kulawa na manya da matasa har zuwa yara. Ga misali, akwai wani matashi da bidiyonsa yaita yawo a kwanakin baya a wannan sashe na midiya wanda bai san ma’anar kalmar “Matasa” ba saida aka fassara masa da “youths”. Wannan abun tir ne da kuma rashin kishi! 

Har yanzu da sauran rina a kaba, domin shuwagabannin mu basa bawa yaren Hausa muhimmanci a sashen karatu musamman a makarantun sakandare. Suna ganin wai harshen Hausa bai iya baza ilimin fasaha da kimiyya ba. Wannan kuskure ne kuma ba daidai ba ne. A gwada, a gani mana.
A tsawon wannan lokaci Hausa da Hausawa sun zama marainiya maras gata.

Bisa abin da na kirɗaɗo ko na kintato dole ne sai mun dawo mun bawa harshen uwa (Hausa) muhimmanci tareda komawa baya wajen amfani da al’adar mu domin cigaban wannan nahiya ta Hausawa ta kowanne fanni domin a fitar da A’i daga Rogo. 

Duk da waƴannan ƙalubalen Harshen Hausa na daya daga cikin harsunan da ke yaɗo, ba a nan Najeriya kadai ba, har ma a cikin kasashen Afrika da Turai baki daya.

A wannan dalili ne nakeso wannan rubutun ya zama matashiya ga duk wani matashin Bahaushe, wanda yake Najeriya da ba wanda yake ciki ba, musulmi ko kirista da yasan akwai wani nauyi da yake kansa dan cigaban wannan yare na Hausa da kuma al’adar Hausawa.

Allah ya taimaki Hausa da Hausawa, sannan ya ƙara sa harshen Hausa ya tumbatsa. Amin.

Ameer Muhammad Harbo daga Jigawan Najeriya.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

13 + nineteen =