‘YAN BOKO HARAM SUN YI GARKUWA DA ‘YAN MATA A SANSANIN ‘YAN GUDUN HIJIRA NA NGALA A JIHAR BORNO

20

Wasu ‘Yan boko haram sun yi garkuwa da mata ‘Yan gudun hijira da suke sansanin ‘Yan gudun hijira na Ngala dake yankin karamar hukumar Gambarou Ngala ta Jihar Borno.

Wata majiya daga hukumomin tsaro ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta yi bayanin cewa yawan wadanda aka yi garkuwa da su ya kai 113 da suka da ‘Yan mata.

Sai dai kuma wata majiya data fito daga sansanin ‘Yan gudun mai suna ‘’Babban Sansani’’ ta shedawa manema labarai cewa  lamarin ya faru a ranar Lahadin data gabata,lokacin da matan suka shiga daji domin neman itacen girki dana sayarwa.

A lokacin ne ‘Yan ta’addar suka kewaye su a dajin Bula Kunte dake yammacin garin Ngala inda suka saki wani dattijo, sannan suka yi awon gaba da mata 319 cikin da hadda ‘Yan mata da kananan yara.

A wan labarin kuma hukumomin tsaro sun sha jan kunnen  ‘Yan gudun hijirar su guji shiga daji domin kaucewa farmakin masu garkuwa da mutane.

Wannan shine garkuwa da mutane mafi girma da aka yi a Jihar tun bayan sace daliban makarantar sakandiren ‘Yan mata ta Chibok su 276 a ranar 14 ga watan Afrilu na shekara ta 2014.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

9 + 14 =