SHUGABAN NAJERIYA BOLA TINUBU YA SAKE YIN KIRA GA JAMI’AN TSARON KASAR SU CETO DALIBAN MAKARANTAR KURIGA

42

Shugaban Najeriya BOLA Ahmed Tinubu ya sake umartar JAMI’AN tsaron kasar su yi duk mai yuyuwa wajen ceto daliban makaranta Firamare da Sakandire Wanda ‘Yan bindinga suka yi garkuwa a Kauyen Kuriga Dake Karamar hukumar Chikun ta Jihar Kaduna.

Ministan yada labarai da wayar da kan Jama’ar Mohammed Idris shine ya sanar da haka ga manema labarai bayan kammala zaman majalisar zartarwa Wanda ya gudana a fadar shugaban kasar Dake Abuja.

ministan yada labaran yace gwamnatin Najeriya baza ta biya kudin fansa ga ‘Yan bindingar domin sakin yaran ba.

Mohammad Idris,ya Kara da cewa gwamnatin Najeriya baza ta zuba Ido a cigaba da yin garkuwa da dalibai a kasar.

yace gwamnatin ta bada umarni ga JAMI’AN tsaro su kubutar da yaran da sauran mutane dake hannun ‘Yan bindinga.

Mohammad Idris, yace idan ta kama gwamnati zata yi amfani da karfin tuwo domin kubutar da yaran, saboda jami’an tsaro ko da yaushe a Shirye suke.

Sama da dalibai 200 ‘Yan bindiga Suka yi garkuwa da su a makarantar Firamare da Sakandire Dake Kauyen Kuriga na karamar hukumar Chikun a Jihar Kaduna.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

2 + nineteen =