MAJALISAR WAKILAN NAJERIYA TA BUKACI A KAWO KARSHEN MATSALAR TSARO A JIHAR KATSINA

13

Majalisar wakilan Najeriya ta bukaci shugaban kasar Bola Ahmed Tinubu ya umarci hukumomin tsaro a Jihar Katsina su tashi haikan wajen fatattakar ‘Yan bindiga a Jihar.

Wannan ya kiran ya biyo bayan wani kudiri da dan majalisar Sada Soli ya gabatar yayin zaman majalisar.

Yayin gabatar da kudirin,Soli ya nuna matukar damuwa dangane da yadda ‘Yan bindiga ke addabar mazauna Jihar Katsina,yana mai cewa hare-hare ‘Yan bindiga a Jihar yayi sanadiyyar rasa rayuka da dama barnata kayayyakin al’umma da yin garkuwa da mutanen da basu ji ba basu gani ba a kowacce rana.

A cewar sa,hukumomin tsaro ya kamata su dauki matakin gaggawa domin magance matsalolin tsaro a Jihar Katsina.

Dan majalisar yayi kira da kara aike da jami’an tsaro masu yawa zuwa yankunan da ke fuskantar hare-hare domin samar da zaman lafiya a yankunan.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

sixteen − 7 =