‘Yan bindiga dauke da makamai a jiya sun kashe wasu mutane 7 ‘yan’uwan juna a wani hari a kauyen Sabon Birni a yankin karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna.
Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar, Samuel Aruwan, ya tabbatar da aukuwar lamarin ga manema labarai yau da safe.
Samuel Aruwan yace akwai yiwuwar adadin wadanda suka mutu ya karu kasancewar jami’an tsaro dake aikin kwantar da tarzoma suna samun sabbin wadanda suka mutu.
Mazauna kauyen sun ce lamarin ya auku a jiya da dare lokacin da ‘yan bindigar suka mamaye kauyen da yawansu suka fara harbi kan mai uwa da wabi.
Wani jagoran al’umma, Bello Musa, ya gayawa manema labarai cewa mazauna kauyen dayawa sun arce daga gidajensu saboda fargabar hari ko kisa a hannun ‘yan fashin dajin.
‘Yan bindigar sun kaddamar da makamancin wannan harin kan wasu kauyuka 13 a mazabar Kerawa a Karamar Hukumar Igabi, inda suka kashe akalla mutane 17.
A wani labarin kuma, an tabbatar da mutuwar mutum guda tare da raunata wani bayan ‘yan fashin daji sun kai hari zuwa gidan wani jami’in yansanda mai suna ASP Aliyu Umar dake yankin Kofar Kwana a Karamar hukumar Zaria ta jihar Kaduna.
An rawaito cewa yan fashin dajin wadanda suka tunkari yankin da yawansu, sun nufi gidan dansandan kai tsaye suna harbi kan mai uwa da wabi.
Da yake zantanwa da manema labarai, ASP Aliyu Umar, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin, yace ga dukkan alamu gidansa kawai suka nufa, kuma ya shaidawa manema labarai cewa sun kashe wani mai suna Abubakar Aliyu yayin da suka jikkata wani dattijo mai suna Abubakar ta hanyar harbinsa a kirji wanda aka garzaya dashi zuwa asibiti.
Aliyu Umar ya kara da cewa ‘yan fashin dajin sun kuma sace wasu shanu da ba a san yawansu ba daga wasu Fulani makotansa a wajen Kofar Kwana ta birnin Zaria.
A cewarsa, yanzu an samu kwanciyar hankali a yankin bayan wasu jami’an yansanda da aka turo sun daidaita lamura.