Gwamna Lalong ya sassauta dokar hana fita a Filato

32

Gwamna Simon Lalong na jihar Plateau ya sassauta dokar kullen da aka sanya a yankin karamar hukumar Jos ta Arewa.

Gwamnan ya bayyana hakan ta cikin sanarwar da daraktan yada labarai da hulda da jama’a na gwamnan, Makut Macham ya fitar a Jos.

Gwamna Lalong ya sanar da cewa, yanzu dokar kullen a Jos ta Arewa zata na aiki ne daga karfe 10 na dare zuwa 6 na safe, farawa daga yau Laraba.

Haka kuma yace an sassauta dokar n, a yayin zaman da kwamitin tsaro ya gudanar a gidan gwamnatin jihar dake Jos, biyo bayan kashe kashen da ake samu a jihar.

Haka kuma yace dokar kullen a karamar hukumar Jos ta kudu da karamar hukumar Bassa har yanzu tana nan daga karfe 10 na dare zuwa 6 na safe.

Kazalika gwamnan ya sassauta dokar da aka sanyawa masu amfani da baburan adedeta sahu.

Gwamnan ya godewa al’ummar jihar Plateau bisa bin dokokin da suke, haka kuma ya roke su da su cigaba da goyawa gwamnati baya, wajen ganin ta dawo da zaman lafiya a jihar.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

nineteen − 2 =