Sanannen matashin dan gwagwarmayar nan Hon. Auwal Yusuf, ya shawarci al’ummar jihar Kaduna cewa idan gwamnan Kaduna Nasiru El-rufai ya basu ‘notice’ a waje to su tashi kawai.
Hon. Auwal, ya bada wannan shawara ce ga al’ummar Kaduna a shafin sa na sada zumuntan facebook, inda yace “Idan malam Nasiru el-rufai ya baku notice cewa ku tashi zai rushe waje to kuyi hakuri ku tashi ku kwashe kayan bukata dana amfanin rayuwar ku domin shi (El-rufai) fa babu imani a cikin lamuran sa ballantana tausayi.
Dan gwagwarmayar ya kara da cewa “Don Allah muma talakawa mu daina taurin kai tunda mun san wannan mutumin babu digon tausayi bare sassauci a zuciyar sa”
”Kwanaki nawa ma suka rage masifar da aka jawo mana da sunan jihadi ta zama tarihi” Inji Hon. Auwal Yusuf.