An ceto mutane tara da aka sace a Katsina

40

An kubutar da mutane tara da aka yi garkuwa da su daga hannun wasu gungun ‘yan fashi a kauyen Kirijam dake karamar hukumar Dandume ta jihar Katsina.

An bayyana hakan ne a wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar, SP Isah Gambo ya sanya wa hannu a madadin kwamishinan ‘yan sanda na jihar.

A cewar wani rahoton ‘yan sanda, ‘yan bindigar sun aukawa kauyen ne da tsakar daren jiya, suna ta harbi a iska, kafin daga bisani suka arce da mutane tara daga kauyen.

Amma, jami’an ‘yansanda na Dandume sun yi wa ‘yan fashin kwanton bauna a daya daga cikin hanyoyin da za su bi, a kauyen Kadawan Maikomo da ke karamar Hukumar Sabuwa.

Jami’an ‘yan sanda sun yi musayar wuta da ‘yan fashin wanda a karshe suka samu nasarar sakin mutane tara da aka sace.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

sixteen + 20 =