CHANZA SHEKAR MATAWALLE: TSAKANIN DOKA DA YA KAMATA

74

Daga Bello Galadi

Rade- radin da akeyi na chanza shekar Mai Girma Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Mohammed (Matawallen Maradun), daga Jamiyyar sa ta PDP zuwa Jamiyyar adawa ta APC, ya tayar da zaune tsaye kuma ya haifar da cece- kuce mai yawa. Wasu suna kallon sauya shekar tashi a matsayin abunda ya sabama doka, wasu kuma suna kallon alamarin a matsayin bai dace ba. Ina cikin rukuni na karshe.

Akwai abubuwa da dama wadanda a al’adance ba laifi bane amma a doka aikata su laifi ne. Hakama, akwai wadansu abubuwan wadanda al’ada ta haramta su amma doka bata hana aikata su ba. Chanza shekar Gwamna mai ci yana daya daga cikin su. 

Shashe na 68(1)(g) da Sashe na 109(1) (g) na Kundin Tsarin Mulki na Nigeria yayi hani ga Sanatoci, da ‘Yan Majalisar Tarayya da na Jihohi akan chanza sheka zuwa wata Jamiyya kafin waadin mulkin su ya kare kuma dokar tayi tanadi na hukunchin yin hakan. Wadanda sukayi dokar, da gangan suka ki sanya mukamin Shugaban Kasa da Mataimakin sa, da Gwamna da Mataimakin sa, a saboda wasu dalilai da su kadai suka sansu. Wannan yana daya daga cikin matsalolin dokokin mu- suna aiki wurin da ake bukatar aikin su.

Hakama, Sashe na 188(1) zuwa (11) na  Kundin Tsarin Mulki bai fadi chanza shegar Gwamna mai ci ba a cikin jerin abubuwan da zasu sa a tsige Gwamna. Akan wannan, chanza shekar Gwamna sanin ya kamata ne ba doka ba.

Matawalle yana da damar yaki chanza sheka domin tsoron rashin tabbas da kuma tunanin kalu balen da zai fuskanta a cikin APC amma ba don tunanin wani tarnaki na doka ba. Yana da damar ya shiga kowace Jamiyyar da yake bukata, daidai da damar da doka ta bashi a karkashin Sashe na 40 na Kundin Tsarin Mulki, kuma saboda ba wata doka a cikin Kundin Tsarin Mulki ko Kundin Dokokin Zabe na Kasa, da suka haramta ma Gwamna mai ci shiga wata Jamiyya kafin waadin mulkin sa ya kare.

Na karanta jawaban masu inkarin cewa Gwamna mai ci baya da damar ya chanza sheka. Kuma na karanta kundin hukunchin da Babbar Kotun Daukaka Kara ta Abuja tayi da kuma umurnin da ta bayar wanda a karkashin su ne aka aiyana Matawalle a matsayin Gwamnan Jihar Zamfara a 2019. Babu wani wuri, ko kai tsaye ko kaikaice, da kotu ta wajabta ma Matawalle tsayawa a cikin PDP har sai waadin mulkin sa ya kare.

A bayyane yake karara, a mahangar doka, cewa Jamiyyar da ta dauki dawainiyar Dan Takara itace taci zabe ba Dan Takarar ba. Amma, da zarar aka rantsar da Gwamna, to Gwamnan ne yake tafiyar da office din ba Jamiyyar sa ba. Maganar Jamiyya ta kau.

Ko wannan raayin nawa daidai yake da doka ko ba daidai yake ba, kotu ce kawai zata warware wannan matsalar. Duk wanda bai ji dadin canza shekar Matawalle ba sai ya garzaya kotu domin a fayyace masa.

A tsarin fayyace dokoki na kasa, anyi matsaya a mahangar doka, cewa “duk lokacin da doka ta fadi wani abu daya, to duk abunda bata fadi ba baya ciki”. A duba shariar OPIA VS. INEC & ANOR. (2014) 3 SCM, 175.

A ra’ayina, ya kamata Matawalle ya tsaya a cikin PDP har zuwa 29th May, 2023. Amma yana da dama a karkashin doka ya shiga Jamiyyar APC ko NRM ko duk Jamiyyar da yake so kuma kowane lokaci. 

Bello Galadi, Tsohon Shugaban Lauyoyi na Jihar Zamfara kuma Shugaban Bello Galadi Foundation.

Za’a iya samun sa a: Muhammadbel_law@yahoo.com and muhammadbellaw80@gmail.com

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

17 − 1 =