Hukumar DSS ta gargadi ‘yan Najeriya dangane da kalaman tayar da rikici

122

Hukumar tsaron farin kaya (DSS) ta bayyana cewa daga yanzu ba za ta kawar da kai daga wasu mutane da ke neman tayar da zaune tsaye a kasarnan ba.

Hukumar ta DSS ta soki abin da ta kira wasu kalamai na marasa son zaman lafiya da ke barazana ga gwamnati da dorewar kasarnan.

Hukumar ta bayyana haka ne a sanarwar da ta fitar jiya Lahadi.

Hukumar ta kara da cewa abin takaici ne mutanen da ake gani da kima suna yin irin wadannan kalamai domin biyan bukatun kashin kansu.

Gargadin yazo ne daidai lokacin da wasu mashahuran ‘yan Najeriya ke kiran ko a tsige shugaban kasa Muhammadu Buhari ko kuma yayi murabus bisa yadda ya kasa kula da matsalar tsaro a fadin kasarnan.

Daga cikin wadanda suka yi wannan kiran akwai limamin cocin nan na Enugu, Ejike Mbaka.

Limamin wanda tsohon dan gani kashen shugaban kasarne, a ranar Alhamis yayi kira ga majalisar kasa da ta shige shugaban kasa Muhammadu Buhari idan ya kasa yin murabus bisa tabarbarewar tsaro a kasarnan.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

thirteen + sixteen =