
Kungiyar Lauyoyi ta Kasa ta maka Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a kotu bisa karin wa’adin aikin da ya yiwa Sufeto Janar na ’Yan sanda, Mohammed Adamu.
Kungiyar ta fara daukar matakin shari’a a Babban Kotun Tarayya dake Lagos.
Wadanda ake karar a karar sun hada da shugaban kasa, da sufeto janar na yansanda da kuma hukumar kula da ayyukan yansanda.
A cikin karar, kungiyar na neman hukuncin shari’a kan yadda shugaban kasa ya tsawaita wa’adin Mohammed Adamu a matsayin Sufeto Janar na ‘yansanda na tsawon watanni uku duk da kasancewar shugaban yansandan a ranar 1 ga Fabrairun da muke ciki ya cika shekaru 35 yana aiki a matsayin dansanda.
A wata sanarwa da ya fitar a yau, shugaban kungiyar lauyoyin, Olumide Akpata, ya ce karin wa’adin ya sabawa kundin tsarin mulki, kuma kungiyar lauyoyin za ta kalubalanci rashin bin doka ko ta halin kaka.