An rufe Majalisar Ghana saboda barkewar cutar corona

25

An rufe majalisar dokokin kasar Ghana tsawon akalla makonni uku saboda karuwar da aka samu ta masamu kamuwa da cutar corona tsakanin ‘yan majalisa da ma’aikatan majalisar.

Kakakin majalisar, Alban Bagbin, ya sanar a jiya cewa majalisar za ta tafi hutu har zuwa ranar 2 ga watan gobe na Maris don ba da damar sanya maganin kashe kwayar cutar a harabar majalisar.

Akalla ‘yan majalisa 17 da ma’aikata 151 sun kamu da cutar ta corona, wacce tuni ta tilastawa‘ yan majalisar takaita zaman ganarwarsu.

Kasar ta tabbatar da jumillar mutane dubu 73 da guda 3 da suka harbu da corona, lamarin da ya jawo mutuwar mutane 482, inda sama da mutane dubu 65 suka warke.

Shugaban kasar Nana Akufo-Addo ya dakatar da manyan tarukan jama’a kamar jana’iza da bukukuwan aure, da kuma kan iyakokin kasar na kasa da na teku sun kasance a rufe tun daga watan Maris na bara.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

seven + 11 =