KAROTA zata kaddamar da saka na’urorin tsaro na bibiyar wajen da abu yake a jikin Kekunan Napep a jihar Kano

76

Manajan Darakta na hukumar KAROTA a jihar Kano, Alhaji Baffa Dan-Agundi yace kwanannan hukumar zata kaddamar da saka na’urorin tsaro na bibiyar wajen da abu yake a jikin kekunan napep a fadin jihar.

Baffa Dan-Agundi ya bayyana haka yayinda yake jawabi ga manema labarai jim kadan bayan ya bayyana a gaban kwamitin ayyuka na majalisar dokokin jihar Kano, domin kare kasafin kudin hukumar na shekarar 2020.

A cewarsa, manufar shirin sanya na’urorin a jikin dukkan kekunan napep dake aiki a jihar shine bibiyar ayyukan bata gari a jihar domin rage ta’addancinsu.

Baffa Dan’Agundi yace hukumar na kokarin fito da shirin aikin gyaran muhalli a matsayin horo ga wadanda suke karya dokokin tuki a fadin jihar.

Ya kara da cewa kwanannan za ayi gyara a dokar data samar da hukumar domin shigar da aikin gyaran muhalli a matsayin horo.

Shugaban hukumar yayi bayanin cewa an warewa hukumar kudi sama da Naira Miliyan 1000 a kasafin kudin badi wanda gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya gabatar kwanannan a gaban majalisar dokokin jihar.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

fourteen + six =