Fadar Shugaban Kasa ta Musanta Cewa Shugaba Buhari ya Zargi Mutanen Borno da Hada Kai Da Boko Haram

42

Babban mataimakin shugaban kasa akan kafafen yada labarai da hulda da jama’a, Mallam Garba Shehu, ya musanta cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya zargi mazauna jihar Borno da hada kai da ‘yan Boko Haram.

Malam Garba Shehu ya fadi haka ne a wani shirin gidan talabijin na kasa, NTA.

Shugaba Buhari yayin ziyarar jaje zuwa Maiduguri a makon da ya gabata, ya bayyana cewa ‘yan Boko Haram baza su iya zuwa birnin Maiduguri da kewaye ba, ba tare da sanayyar mutanen gari ba.

Sai dai Garba Shehu yace an yiwa kalaman shugaban kasar mummunar fassara, inda ya kara da cewa ya sha suka a kafafen sada zumunta saboda kalaman.

Mai bawa gwamnan jihar Borno shawara akan dabarun hulda da jama’a, Mallam Isa Gusau, wanda shima ya halarci shirin tare da Garba Shehu, ya nuna takaici bisa zargin Shugaban Kasa na cewa Boko Haram na samun nasara sanadiyyar hadin gwiwa da jama’ar gari.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

3 + 14 =