Gwamnatin Tarayya Ta Aika Da Kayan Agaji Zuwa Garin Auno a Jihar Borno

40

Gwamnatin Tarayya ta aika da kayan tallafi ga mazauna garin Auno, da ke kusa da birnin Maigudurin Jihar Borno, wanda a kwanakinnan masu tada hare hare suka kai masa hari.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kai ziyarar jaje zuwa birnin Maiduguri, makon da ya gabata, bisa kisan mutane 30 da mayakan suka yi.

Ma’aikatar Jin Kai, Kula da Iftila’I da walwala, tare da hukumar cigaban yankin Arewa maso Gabas, sun raba kayan abinci da wanda ba na abinci ba, ga mutanen garin Auno.

Manajan Darakta na hukumar, Mohammed Alkali, yace kayan agajin sun hada da barguna 5000, da buhunhunan wake 1000  da katifu 1000 da katan 200 na man girki da buhunhunan shinkafa 1000 da katan 50 na tumaturin gwangwani da katan 50 na maggi da kuma tabarmai 1000.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

1 × 4 =