Yansanda Da Jami’an Civil Defense Sun Tsaurara Tsaro A Kusa Da Ofisoshin Jakadancin Amurka Da Na Birtaniya A Abuja

36

Yansanda da jami’an hukumar civil defense sun tsaurara tsaro a kusa da ofisoshin jakadancin Amurka da na Birtaniya a Abuja, a wani mataki na mayar da martani dangane da fargabar cewa za a iya kai musu hari daga kungiyoyin dake marawa Iran baya wajen ramuwar kisan babban sojinta, Qassem Soleimani.

An dai kashe Shugaban manyan sojojin Iran, Qassem Soleimani, a wani harin saman Amurka a kusa da filin jiragen saman Bagadaza a ranar 3 ga watan Janairu.

Kisansa ya jawo tabarbarewar alaka tsakanin kasashen biyu, inda Shugaban addinin Iran, Ayatollah Ali Khamenei, yayi alkawarin cewa kasar zata rama harin.

Kasar ta Iran a ranar Laraba ta kaddamar da harin makamai masu linzami a kan sansanonin sojin saman Amurka guda 2 dake Iraqi inda sojin Amurka suke zama.

Jami’an tsaro sun katange guraren domin dakile kowane hari akan ofisoshin jakadancin Amurka da na Birtaniya, wadanda ke kusa da juna, tun bayan kisan na Qassem Soleimani tare da Shugaban dakarun fararen hular Iraqi, Abu Mahdi al-Muhandis, a harin saman na Bagadaza.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

13 + nine =