Shugaba Buhari Ya Nemi Hadin Gwiwar Kasashen ECOWAS Domin Yakar Ta’addanci

22

Shugaban Kasa Muhammad Buhari ya bukaci hadin gwiwar kasashen da suke karkashin kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika, wato ECOWAS, domin yakar ta’addanci.

Shugaba Buhari ya bayyana haka ne a lokacin taron kungiyar ECOWAS, karo 56 wanda aka gudanar a Abuja.

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce halin da ake ciki a yanzu na hare-hare yan Boko Haram yana sake tunatar da shugabanni kungiyar ECOWAS halin da kasashen ke ciki, saboda haka akwai bukatar duk wani dan kasa mai san zaman lafiya da ya taho domin ya bada gudunmawa.

Kazalika shugaba Buhari a lokacin taron ya umarci ayi shiru na wasu yan mintuna domin tunawa da sojoji guda 70 da ‘yan kungiyar suka kashe a kasar Niger.

A jawabinsa yayin bude taron shugaban kasar Niger, Muhammad Issoufu, wanda kuma shine shugaban kungiyar yayi nuni da irin illolin da mayakan kungiyar Boko Haram suke yi ga cigaban tattalin arzikin kasashen.

Shima a jawabinsa, shugaban hukumar ECOWAS Jean-Claude Kassi Brou, ya yabawa mambobin kungiyar bisa yadda suke kokarin ganin sun bunkasa cigaban tattalin arzikin kasashen.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

4 × 3 =