Senegal: Sonko da Diomaye sun shaki iskar ‘yanci

22

Jagoran adawar Senegal Ousmane Sonko ya shaki iskar ‘yanci daga kurkuku, a wani bangare na afuwar da shugaban kasar ya yi wa ‘yan siyasa, kwanaki kalilan gabanin zaben shugaban kasar, lamarin da ya jefa magoya bayansa cikin murna da sowa suna daga tututa da hotunansa a fadin kasar.

Lauyansa Bamba Cisse, ya bayyana cewa an saki Sonko da na hannun damansa Bassirou Diomaye Faye, bayan tsare su da gwamnatin Macky Sall ta yi a gidan yari tun cikin watan Yulin bara.

Jam’iyyarsu ta adawa ta tsayar da Bassirou Diomaye Faye a matsayin ‘dan takarar shugaban kasa, bayan da kotun tsarin mulkin kasar ta haramta wa Ousmane Sonko shiga zaben, gabanin daure su.

A ranar 24 ga wannan wata na Maris za a gudanar da zaben kasar, bayan kwarbai na jeka-dawo da aka sha tun lokacin da shugaba Sall ya dage zaben watan Fabarairun da ya gabata.

DW

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

6 − three =