GWAMNATIN KASAR VENEZUELA TA SHIRYA GUDANAR DA ZABEN SHUGABAN KASAR RANAR 28 GA WATAN YULIN WANNAN SHEKARA

13

Gwamnatin kasar Venezuela ta shirya gudanar da zaben shugaban kasar a ranar 28 ga watan Yuli na wannan shekara.

Shugaban kasar Nicolas Maduro, wanda ke shugabancin kasar tsawon shekaru 11 ya bayyana a fili cewa ana sa ran zai sake neman shugabancin kasar.

A shekarar data gaba ne,gwamnatin kasar da kuma bangaran adawa a kudancin Amurka suka amince a gudanar da zaben shugaban kasar a wannan shekara tare da gayyato masu sa ido daga kasashen duniya.

A zabuka da suka gudana a shekarar 2018, lokacin da aka bayyana Mista Maduro a matsayin wanda ya lashe zaben ‘Yan kasar sun bayyana shakkun kan sahihancin zaben.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

fifteen + 17 =