Yayin da ake fuskantar barazanar ta’addanci a Abuja, Amurka ta bukaci ‘yan uwan ma’aikatanta mazauna birnin da su fice.
Wannan yana kunshe ne a cikin sabuwar sanarwar shawarar tafiye-tafiye da ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ya fitar.
An ba da sanarwar farko na irin wannan gargadi a ranar Lahadin da ta gabata bayan da akalla ofisoshin jakadancin kasashen waje tara suka nuna fargabar cewa za a iya kai hare-hare a Abuja.
Daga cikin kasashen da suka nuna fargabar sun hada da Burtaniya, da Kanada, da Australia, da Ireland, da Denmark, da Bulgaria, da Indiya da kuma Jamus.
Amma Gwamnatin Tarayya ta tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa akwai tsaro da zaman lafiya a babban birnin kasar.
Duk da wannan, an samu rahotannin da ba a tabbatar da su ba da ke cewa ‘yan kasashen waje dayawa na ficewa daga kasar.
A jiya, aka rufe daya daga cikin manyan kantunan Abuja, har sai sai abinda hali yayi, saboda rashin tsaro.