Hukumar tsaron fararen hula civil defence a jihar Jigawa ta bayyana cewa mutane 5 ne suka samu raunuka sakamakon fashewar tukunyar gas da ake kyautata zaton ta fasa kwauri ce a karamar hukumar Babura ta jihar.
Kakakin rundunar, Adamu Shehu, wanda ya tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na kasa afkuwar lamarin a yau a Dutse, ya kara da cewa fashewar ta kuma lalata shaguna da gidaje.
Adamu Shehu ya ce lamarin ya faru ne a jiya da misalin karfe 9 na dare bayan da jami’an tsaro masu bincike a yankin suka tsayar da wata babbar mota da ke dauke da tukwanen gas guda 25.
Ya yi zargin cewa direban motar ya ki tsayawa ne saboda haka jami’an tsaro suka bi shi, wanda hakan ya sa daya daga cikin tukwanen ta fado daga motar kuma ta kama da wuta nan take.
Kakakin ya kara da cewa motar ta fito ne daga jamhuriyar Nijar kuma ta nufi Hadejia a jihar Jigawa.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Lawan Shiisu Adam, shi ma ya tabbatar da faruwar lamarin.
Shiisu Adam ya ce shaguna 17 da gidaje biyar ne suka lalace sakamakon gobarar da fashewar ta haddasa.