Mutane 19 sun mutu a hadarin mota a Kano

60

Wani mummunan hatsarin mota da ya afku a kauyen Bagauda da ke kusa da harabar makarantar koyon aikin lauya ta kasa dake Kano a jiya, ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 19, yayin da wasu 26 suka samu raunuka.

Wani jariri da mahaifiyarsa, manyan mata, da kuma dattawa maza na cikin wadanda suka mutu a hadarin.

Hadarin ya rutsa da fasinjoji 45 na wasu motocin bas guda biyu na haya inda suka yi karo da juna suka kama da wuta.

Kwamandan hukumar kiyaye haddura ta kasa (FRSC) reshen jihar Kano, Zubairu Mato, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai.

Zubairu Mato ya dora laifin kan gudun da ya wuce hankali da kuma tukin ganganci.

A cewar kwamandan reshen, an kai wadanda suka jikkata zuwa babban asibitin Kura yayin da aka mika gawarwakin wadanda suka mutu ga ‘yan uwansu a ofishin ‘yan sanda na Bebeji.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

1 × 3 =