
Gwamnatin tarayya ta ce tana hada kai da jami’an tsaro domin tabbatar da ingantaccen tsaro a makarantun sakandiren tarayya gabannin bude su a ranar 12 ga watan Satumba.
Karamin Ministan Ilimi, Goodluck Opiah ne ya bayyana hakan a yayin wani taron manema labarai da ya kira domin shirye-shiryen bikin ranar kare ilimi ta duniya daga hare-hare ta bana.
Idan za a iya tunawa dai, a watan Yuli ne Gwamnatin Tarayya ta rufe Kwalejin Gwamnatin Tarayya ta Kwali da sauran Makarantu a Babban Birnin Tarayya saboda fargabar harin ‘yan bindiga.
Ministan ya ce rufewar ba ta dindindin ba ce, don haka an kusa bude makarantu kuma Kwalejin Gwamnatin Tarayya ta Kwali ita ma tana cikin wadanda za a bude.
Goodluck Opiah ya kuma ce an fara bikin ranar kare ilimi ta duniya daga hare-hare a kasar Qatar.
Ya kara da cewa wasu kasashe 62 ne suka dauki nauyin samar da ranar a babban taron zauren Majalisar Dinkin Duniya karo na 76 a shekarar 2020.
Goodluck Opia ya yi kira ga masu ruwa da tsaki da su kare ilimi daga yanayin rashin tsaro da tashin hankali da rigingimu.