Gwamnatin Jigawa za ta raba awakin Sahel

54

Gwamnatin jihar Jigawa ta kammala shirin rabon awakin Sahel na gwaji a fadin jihar nan.

Kwamishinan ayyuka na musamman kuma mai rikon kujerar ma’aikatar aikin gona ta jiha, Alhaji Auwal Danladi Sankara ya sanar da hakan a lokacin da ya kai ziyarar duba awakin a karamar hukumar Birniwa.

Yace shirin na daga cikin yarjejeniyar da aka cimma tsakanin gwamnatin jihar Jigawa da ta jihar Zindar a jamhuriyar Nijar a farkon makon daya gabata.

Kwamishinan yace gwamnatin jihar Jigawa ta kuduri aniyar sayen awakin na yankin Sahel guda 645 domin inganta yanayin kiwon akuyoyi da kuma bunkasar tattalin arzikin jihar nan.

Daga bisani kwamishinan ya kuma duba wasu shanu da za a raba a karamar hukumar ta Birniwa.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

12 + three =