Gwamnatin tarayya ta tallafawa wadanda ambaliya ta shafa a Jigawa

46

Gwamnatin tarayya ta jajantawa wadanda ambaliyar ruwa ta rutsa da su da wadanda suka mutu sakamakon ruftawar gine-gine a jihar Jigawa.

Ministar jin kai da walwala da ci gaban al’umma, Hajiya Sadiya Umar Farouk, ta bayyana haka a lokacin da ta kai wa Gwamna Muhammad Badaru Abubakar ziyarar ban girma a gidan gwamnati dake Dutse.

Ta bayyana cewa, sun je jihar ne domin gabatar da kayayyakin abinci da kayayyakin gini ga wadanda abin ya shafa kamar yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarta.

Sadiya Umar Farouk ta kara da cewa tuni tawagar hukumar bada agajin gaggawa ta kasa NEMA ta isa jihar domin tuntubar hukumar bada agajin gaggawa ta jihar tare da tantance adadin wadanda abin ya shafa da kuma asarar da aka samu.

Da yake mayar da martani, Gwamna Muhammad Badaru Abubakar ya bayyana jin dadinsa ga ma’aikatar jin kai ta tarayya bisa samar da ayyukan yi ga matasa da kuma baiwa mata damar yin sana’o’i domin dogaro da kai.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

two × 2 =