Gwamnati ta hana shigo da layikan waya

58

Gwamnatin tarayya ta ce ta hana shigo da layikan waya da ake amfani da su a wayoyin hannu.

Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Isa Ali Pantami, ya fada jiya a wani taron masana’antu cewa yanzu haka ana samar da layukan a Najeriya.

Ya kara da cewa haramcin na daya daga cikin kokarin gwamnatin tarayya na bunkasa masana’antun cikin gida biyo bayan kaddamar da masana’antar layin waya a watan Yuni a Legas.

Ya bayyana cewa Nijeriya a matsayinta na kasa mafi yawan al’umma a Afirka, bai kamata a rika shigo da kayayyakin da za a iya kerawa a cikin gida ba, ya kara da cewa gwamnati na son bangaren fasahar Najeriya ya zama mai dogaro da kai da kashi 80 cikin 100 nan da shekarar 2025.

Masu lura da al’amura sun ce samun layin waya da ake sarrafawa a cikin kasa na iya rage farashin layin, amma kasancewar kamfani daya ne ke sarrafa shi, hakan zai iya zama matsala.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

17 − 6 =