Buhari ya tafi ziyarar ta’aziyya zuwa Hadaddiyar Daular Larabawa

48

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bar Abuja a yau zuwa Hadaddiyar Daular Larabawa domin ziyarar ta’aziyya.

Shugaba Buhari zai gana da sabon shugaban Hadaddiyar Daular Larabawa, Sheikh Mohamed bin Zayed Al Nahyan, domin mika sakon ta’aziyyarsa bisa rasuwar tsohon shugaban kasa kuma Sarkin Abu Dhabi, Sheikh Khalifa bin Zayed Al Nahyan.

Kakakin shugaban kasa, Garba Shehu, shine ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a yau.

A cewar mai magana da yawun shugaban kasar, shugaba Buhari zai kuma mika sakon taya murna ga sabon shugaban kasar tare da sabunta tsohuwar dangantakar abotar dake tsakanin Najeriya da Daular ta Larabawa.

Shugaban kasar, a sakon taya murna da ya aika tun a baya zuwa ga sabon shugaban Hadaddiyar Daular Larabawa, ya nanata kyakykyawar alaka tsakanin Najeriya da Daular.

Yayi nuni da cewa hadin kai tsakanin gwamnatocin biyu ya taimakawa Najeriya wajen gano kadarorin sata da bankado kudaden ‘yan ta’adda.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

four + seven =