Gwamnan Jihar Jigawa Muhammad Badaru Abubakar ya bayar da umarnin gaggauta mayar da shugaban karamar Yankwashi, Alhaji Mubarak Ahmed Achilafiya.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa dauke da sa hannun kwamishinan kananan hukumomi, Alhaji Kabiru Hassan Sugungun.
A baya an bayar da labarin cewa majalisar dokokin jihar Jigawa ta dakatar da shugaban karamar hukumar Yankwashi na jihar har sai abinda hali yayi, bisa zargin rashin biyayya ga shugaban jam’iyyar APC na jihar.
Shugaban kwamitin yada labarai na majalisar, dan majalisa mai wakiltar mazabar Kafin Hausa, Honorabul Muhammad Na’im ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Dutse.
Ya ce an dakatar da shugaban karamar hukumar ne bisa zargin cutarwa da yada labaran karya kan shugaban jam’iyyar APC na jihar, Aminu Sani Gumel.
Kazalika ya bayyana cewa majalisar ta kuma samu jerin korafe-korafe na almubazzaranci da dukiyar al’umma da kuma cin zarafin al’umma daga shugabannin kananan hukumomi takwas.
Sai dai daya daga cikin shugabannin kananan hukumomin, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana zargin a matsayin na karya kuma maras tushe. Ya ce zargin bita da kulli ne kawai irin na siyasa.